Loading...
Language: Hausa
Idan dare ya yi [wato, a Magariba], ku hana yaran ku [fita] saboda a irin wannan lokaci shaidanu suna bazuwa. Bayan wani lokaci ya wuce, ku bar su. Ku rufe ƙofofinku ku ambaci sunan Allah, domin lallai shaidan ba ya buɗe rufaffiyar ƙofa, ku ɗaure salkunan ruwanku ku ambaci sunan Allah, ku rufe kwanukan ku da kowane abu ku ambaci sunan Allah kuma ku kashe fitilun ku.'
Reference: Bukhari: 5623