Loading...
Language: Hausa
وَجَّهْتُ وَجْهِيَ لِلَّذِي فَطَرَ السَّمَوَاتِ وَالْأَرْضَ حَنِيفًا وَمَا أَنَا مِنَ الْمُشْرِكِينَ، إِنَّ صَلَاتِي، وَنُسُكِي، وَمَحْيَايَ، وَمَمَاتِي لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ، لَا شَرِيكَ لَهُ وَبِذَلِكَ أُمِرْتُ وَأَنَا مِنَ الْمُسْلِمِينَ اَللَّهُمَّ أَنْتَ الْمَلِكُ لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ، أَنْتَ رَبِّي وَأَنَا عَبْدُكَ، ظَلَمْتُ نَفْسِي وَاعْتَرَفْتُ بِذَنْبِي فَاغْفِرْ لِي ذُنُوبِي جَمِيعًا إِنَّهُ لَا يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إِلَّا أَنْتَ، وَاهْدِنِي لِأَحْسَنِ الْأَخْلَاقِ لَا يَهْدِي لِأَحْسَنِهَا إِلَّا أَنْتَ، وَاصْرِفْ عَنِّي سَيِّئَهَا، لَا يَصْرِفُ عَنِّي سَيِّئَهَا إِلَّا أَنْتَ لَبَّيْكَ وَسَعْدَيْكَ، وَالْخَيْرُ كُلُّهُ بِيَـدَيْكَ، وَالشَّـرُّ لَيْسَ إِلَيْـكَ، أَنَا بِكَ وَإِلَيْكَ، تَبارَكْتَ وَتَعَالَيْتَ، أَسْتَغْفِرُكَ وَأَتوبُ إِلَيْكَ
Wajjahtu wajhiya lilladhee fataras-samawaati wal-arda haneefan wa maa ana minal-mushrikeen, inna salaatee wa nusukee wa mahyaaya wa mamaatee lillaahi rabbil-’alameen, laa shareeka lahu wabi dhaalika umirtu wa-ana minal-muslimeen. Allaahumma antal-maliku laa ilaaha illaa anta. anta rabbee wa-anaa ‘abduka, dhalamtu nafsee wa’taraftu bidhanbee faghfir lee dhunoobee jamee’an innahu laa yaghfirudh-dhunooba illaa anta. wahdinee li-ahsanil-akhlaaqi laa yahdee li-ahsaniha illaa anta, wasrif ‘annee sayyiaha laa yasrifu ‘annee sayyiaha illaa anta, Labbayka wa sa’dayka, wal-khayru kulluhu biyadayka, washsharru laysa ilayka, ana bika wa-ilayka, tabarakta wa ta’alayta, astaghfiruka wa atoobu ilayk
Na fuskantar da fuskata ga Wanda ya halicci sammai da ƙasa, ina mai karkata zuwa ga gaskiya kuma ni ba na cikin masu shirka. Lallai sallata, layyata, rayuwata da mutuwata na Allah ne, Ubangijin talikai, ba shi da abokin tarayya; da wannan aka umarce ni kuma ni na farkon Musulmai. Ya Allah, Kai ne Sarki babu abin bautawa da gaskiya sai Kai. Kai ne Ubangijina kuma ni bawanka ne, na zalunci kaina kuma na amsa zunubina, don haka ka gafarta mini dukkan zunubaina domin babu mai gafarta zunubai sai Kai. Ka shiryar da ni zuwa ga mafi kyawun halaye domin babu mai shiryarwa zuwa gare su sai Kai, kuma ka kawar mini da miyagun halaye domin babu mai kawar mini da su sai Kai. Gani nan na amsa kiranka, kuma ina farin cikin yi maka hidima. Dukkan alheri yana hannunka kuma sharri ba ya zuwa gare ka. Ina rayuwa da ikonka kuma zan koma gare ka. Tsarki ya tabbata a gare ka kuma ka ɗaukaka, ina neman gafararka kuma ina tuba zuwa gare ka.
Reference: Muslim: 771