Loading...
Language: Hausa
Ayesha (RA) ta ce, ban sami Manzon Allah (ﷺ) a gado ba wani dare. (A cikin duhu) na neme shi. Sai hannuna ya taɓa tafin ƙafarsa. Yana cikin sujada kuma ƙafafunsa a tsaye. Yana cewa:
اَللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوْذُ بِرِضَاكَ مِنْ سَخَطِكَ، وَبِمُعَافَاتِكَ مِنْ عُقُوبَتِكَ، وَأَعُوْذُ بِكَ مِنْكَ، لَا أُحْصِيْ ثَنَاءً عَلَيْكَ، أَنْتَ كَمَا أَثْنَيْتَ عَلَى نَفْسِكَ
Allaahumma 'innee 'a'oodhu biridhaaka min sakhatik, wa bimu'aafaatika min 'uqoobatik wa 'a'oodhu bika minka, laa 'uhsee thanaa'an 'alayka, 'Anta kamaa 'athnayta 'alaa nafsik
Ya Allah, ina neman tsari da yardarKa daga fushinKa, da afuwarKa daga uƙubarKa, kuma ina neman tsari da Kai daga gare Ka. Ba zan iya lissafin yabo a gare Ka ba. Kai kamar yadda Ka yabi KanKa ne.
Reference: Muslim: 486, Sahih (Albani). Tirmidhi: 3566