Loading...
Language: Hausa
Annabi (ﷺ) ya kasance yana faɗin wannan addu'a bayan kowane sallar farilla:
لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيْكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، اَللَّهُمَّ لَا مَانِعَ لِمَا أَعْطَيْتَ، وَلَا مُعْطِىَ لِمَا مَنَعْتَ، وَلَا يَنْفَعُ ذَا الْجَدِّ مِنْكَ الْجَدُّ
Laa ilaaha ill-Allahu wa'hdahu laa shareeka lahu, lahul-mulku wa lahul-'hamdu wa huwa ‛alaa kulli shay’in qadeer, Allaahumma laa maani‛a li maa a‛tayta, wa laa mu‛tiya li maa mana‛ta wa laa yanfa‛u dhal-jaddi minkal-jaddu
Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai, ba Shi da abokin tarayya, gare Shi mulki yake kuma gare Shi yabo yake kuma Shi Mai iko ne akan komai. Ya Allah, babu mai hana abin da Ka bayar kuma babu mai bayar da abin da Ka hana, kuma dukiya ko girma ba ya amfanar kowa, kamar yadda daga gare Ka ne dukkan dukiya da girma.
Reference: Bukhari: 844