Loading...
Language: Hausa
Anas bin Malik (RA) ya ruwaito cewa Manzon Allah (ﷺ) ya ce: "Duk wanda ya yi sallar Asuba a jam'i, sannan ya zauna yana ambaton Allah har rana ta fito, sannan ya yi Raka'a biyu, to yana da lada kamar na Aikin Hajji da Umrah." Ya ce: "Manzon Allah (ﷺ) ya ce: Cikakke, cikakke, cikakke (Hajji da Umrah)."
Reference: Hasan (Albani). Tirmidhi: 586