Loading...
Language: Hausa
Manzon Allah (ﷺ) ya kasance yana cewa Bismillah yayin hawa abin hawa, yana faɗin sauran bayan zama:
اَلْحَمْدُ لِلَّهِ، سُبْحَانَ الَّذِي سَخَّرَ لَنَا هَذَا وَمَا كُنَّا لَهُ مُقْرِنِيْنَ وَإِنَّا إِلَى رَبِّنَا لَمُنْقَلِبُوْنَ، اَلْحَمْدُ لِلَّهِ، اَلْحَمْدُ لِلَّهِ، اَلْحَمْدُ لِلَّهِ، اللَّهُ أَكْبَرُ، اللَّهُ أَكْبَرُ، اَللّهُ أَكْبَرُ، (لَا إِلٰهَ إِلَّا أَنْتَ) سُبْحَانَكَ، إِنِّي ظَلَمْتُ نَفْسِيْ فَاغْفِرْ لِي فَإِنَّهُ لَا يَغْفِرُ الذُّنُوْبَ إِلاَّ أَنْتَ
Alhamdu lillaah. Subhaanal-ladhee sakhkhara lanaa haadhaa wa maa kunnaa lahu muqrineen. Wa 'innaa 'ilaa Rabbinaa lamunqaliboon. Alhamdu lillaah, alhamdu lillaah, alhamdu lillaah, Allahu 'Akbar, Allahu 'Akbar, Allahu 'Akbar, (laa ilahaa 'illaa 'Anta) subhaanaka 'innee dhalamtu nafsee faghfir lee, fa'innahu laa yaghfirudh-dhunooba 'illaa 'Anta
Godiya ta tabbata ga Allah. Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya hore mana wannan alhali ba mu kasance masu iya mallakarsa ba. Kuma lallai mu zuwa ga Ubangijinmu masu komawa ne. Godiya ta tabbata ga Allah (sau 3). Allah Mai girma (sau 3). Tsarki ya tabbata a gare Ka. Ya Allah, na zalunci kaina. Gafarta min, domin babu mai gafarta zunubai sai Kai.
Reference: Sahih (Albani). Tirmidhi: 3446