Loading...
Language: Hausa
An ruwaito daga Amr Ibn Shuaib (RA) daga kakansa ta wurin mahaifinsa, Annabi (ﷺ) ya ce, “Addu'a mafi kyau ita ce addu'a a ranar Arafa. Addu'a mafi kyau da ni da magabata muka karanta ita ce -
لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ
Laa 'ilaaha 'illAllahu wahdahu laa shareeka lahu, lahul-mulku wa lahul-hamdu wa Huwa 'alaa kulli shay'in Qadeer
Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai, ba Ya da abokin tarayya, Mulki naSa ne kuma yabo naSa ne kuma Shi Mai ikon yi ne a kan komai.
Reference: Hadisin Hasan ne. Tirmidhi, 3585