Loading...
Language: Hausa
Annabi (ﷺ) ya ƙara da cewa: Mutumin da ya ce:
أَسْتَغْفِرُ اللَّهَ الْعَظِيمَ الَّذِيْ لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ وَأَتُوبُ إِلَيْهِ
Astaghfirulla-hal adhemal-ladhee laa ilaaha illaa huwal hayyul qayyoomu wa atoobu ilayhi
Ina neman gafarar Allah Mai girma, wanda babu abin bautawa da gaskiya sai Shi, Rayayye, Madawwami, kuma na tuba zuwa gare Shi. Allah zai gafarta masa ko da kuwa shi ne wanda ya gudu yayin ci gaban runduna." [1] Ya (ﷺ) ya ce: "Mafi kusa da Ubangiji yake zuwa ga bawanSa shi ne a tsakiyar dare, saboda haka idan za ku iya kasancewa daga cikin waɗanda ke ambaton Allah a wannan lokacin, to ku kasance haka." [2] Ya (ﷺ) kuma ya ce: "Mafi kusa da bawa yake ga Ubangijinsa shi ne lokacin da yake sujjada, saboda haka ku yi addu'a da yawa a ciki." [3] Ya (ﷺ) kuma ya ce: "Lallai zuciyata tana shagala, kuma lallai ina neman gafarar Allah sau ɗari a rana." [4]
Reference: [1] Sahih (Albani). Abu Dawud: 1517 [2] Sahih (Albani). Tirmidhi: 3579 [3] Muslim: 482 [4] Muslim: 2702