Loading...
Language: Hausa
Annabi (ﷺ) ya ce, Idan wani yana tsoron haɗuwa da maƙiyi ko masu mulki, to ya ce:
اَللَّهُمَّ رَبَّ السَّمَوَاتِ السَّبْعِ وَرَبَّ الْعَرْشِ الْعَظِيْمِ كُنْ لِي جَارًا مِنْ فُلَانِ بْنِ فُلَانٍ، وَأَحْزَابِهِ مِنْ خَلَائِقِكَ (وَمِنْ شَرِّ خَلْقِكَ كُلِّهِمْ جَمِيْعًا) أَنْ يَفْرُطَ عَلَيَّ أَحَدٌ مِنْهُمْ أَوْ يَطْغَى عَزَّ جَارُكَ وَجَلَّ ثَنَاؤُكَ وَلَا إِلٰهَ إِلَّا أَنْتَ
Allaahumma Rabbas-samawaatis-sab'i, wa Rabbal-'Arshil-'Adheem, kun lee jaaran min [here you mention the person's name], wa 'ahzaabihi min khalaa'iqika, (wa min sharri khalqika kullihim jami'an) 'an yafruta 'alayya 'ahadun minhum 'aw yatghaa, 'azza jaaruka, wajalla thanaa'uka, wa laa 'ilaaha 'illaa 'Anta
Ya Allah, Ubangijin sammai bakwai, Ubangijin Al'arshi Mai Girma, kasance Mai ba ni kariya daga [an nan ku ambaci sunan mutumin], da mataimakansa daga halittunKa, (da daga sharrin dukkan halittunKa baki ɗaya) kada ɗayansu ya yi gaggawar cutar da ni ko ya keta haddi. KariyarKa tana da girma, kuma yabonKa yana da ɗaukaka. Babu abin bautawa da gaskiya sai Kai.
Reference: Sahih (Albani). Sahih At-Targhib: 2237, Adabul Mufrad: 707