Loading...
Language: Hausa
Ibn 'Abbas (RA) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya kasance yana faɗin waɗannan kalmomi a lokutan haɗari ko tsanani:
لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، الْعَظِيْمُ الْحَلِيْمُ لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، رَبُّ الْعَرْشِ الْعَظِيْمِ لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، رَبُّ السَّمَاوَاتِ، وَرَبُّ الْأَرْضِ، وَرَبُّ الْعَرْشِ الْكَرِيمِ
Laa 'ilaaha 'illAllaahul-'Adheemul-Haleem, laa 'ilaaha 'illAllaahu Rabbul-'Arshil-'Adheem, laa 'ilaaha 'illAllaahu Rabbus-samaawaati wa Rabbul-'ardhi wa Rabbul-'Arshil-Kareem
Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Mai Girma, Mai Haƙuri. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Ubangijin Al'arshi Mai Girma. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Ubangijin sammai da Ubangijin ƙasa, da Ubangijin Al'arshi Mai Daraja.
Reference: Bukhari 7431