Loading...
Language: Hausa
An ruwaito daga Abu Huraira (RA): Annabi (ﷺ) ya ce, "Idan kuka ji kukan zakaru, ku roƙi Allah falalarSa, domin (kukan nasu yana nuna) sun ga mala'ika. Kuma idan kuka ji kukan jakuna, ku nemi tsari daga Allah daga Shaiɗan, domin (kukansu yana nuna) cewa sun ga Shaiɗan."
Reference: Bukhari: 3303