Loading...
Language: Hausa
An ruwaito daga Abu Huraira (RA): Manzon Allah (ﷺ) ya ce: Iska tana daga rahamar Allah; tana zuwa da rahama, kuma tana zuwa da azaba. Don haka idan kuka ga tana kaɗawa, kada ku zage ta; (Maimakon haka) ku nemi alherinta daga Allah, kuma ku nemi tsari (daga Allah) daga sharrinta.
Reference: Sahih (Albani). Abu Dawud 5097