Loading...
Language: Hausa
An ruwaito daga Anas Ibn Malik ya ce: "Mun kasance tare da Manzon Allah (ﷺ), sai ruwan sama ya sauka a kanmu. Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ɗage wani sashi na tufafinsa domin ruwan ya taɓa jikinsa. Muka ce, 'Ya Manzon Allah! Me ya sa ka yi haka?' Ya ce, 'Domin yanzu-yanzun nan ya fito daga wurin Ubangijinsa mai girma!'"
Reference: Muslim: 898