Loading...
Language: Hausa
An ruwaito daga Abu Huraira (RA): Annabi (ﷺ) ya ce, "Ku ce Amin" lokacin da Liman ya faɗi shi kuma idan Amin na ɗaya daga cikinku ya dace da na mala'iku to za a gafarta masa dukkan zunubansa da suka gabata." [1] An ruwaito daga Abu Huraira (RA): Manzon Allah (ﷺ) ya ce, "Ku ce Amin" lokacin da Liman ya ce 'Ghairil maghdubi 'alaihim walad daalleen' (ba hanyar wadanda aka yi wa fushi ba (kamar Yahudawa) ko wadanda suka bace (kamar Kiristoci); duk zunuban mutumin da fadinsa (Amin) ya dace da na mala'iku, za a gafarta masa". [2]
Reference: [1] Bukhari: 780 [2] Bukhari: 782