Loading...
Language: Hausa
Jibrilu (AS) ya ce wa Annabi (ﷺ) don kare kansa daga shaiɗan:
أَعُوْذُ بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّاتِ الَّتِي لَا يُجَاوِزُهُنَّ بَرٌّ وَلَا فَاجِرٌ مِنْ شَرِّ مَا خَلَقَ، وَبَرَأَ وَذَرَأَ، وَمِنْ شَرِّ مَا يَنْزِلُ مِنَ السَّمَاءِ، وَمِنْ شَرِّ مَا يَعْرُجُ فِيهَا، وَمِنْ شَرِّ مَا ذَرَأَ فِي الْأَرْضِ، وَمِنْ شَرِّ مَا يَخْرُجُ مِنْهَا، وَمِنْ شَرِّ فِتَنِ اللَّيْلِ وَالنَّهَارِ، وَمِنْ شَرِّ كُلِّ طَارِقٍ إِلَّا طَارِقًا يَطْرُقُ بِخَيْرٍ يَا رَحْمَنُ
A'oodhu bikalimaatil-laahit-taammaatil-latee laa yujaawizuhunna barrun wa laa faajirum min sharri maa khalaqa, wa bara'a wa dhara'a, wa min sharri maa yanzilu minas-samaa'i, wa min sharri maa ya'ruju feehaa, wa min sharri maa dhara'a fil-'ardhi, wa min sharri ma yakhruju minhaa, wa min sharri fitanil-layli wan-nahaari, wa min sharri kulli taariqin 'illaa taariqan yatruqu bikhayrin yaa Rahmaan
Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku, waɗanda babu wani mai biyayya ko fasiƙi da zai iya tsallake su, daga sharrin abin da Ya halitta, da abin da Ya zubar, da abin da Ya ƙaga. Da sharrin abin da ke sauka daga sama da abin da ke hawa cikinta. Da sharrin abin da ke bazuwa a ƙasa da sharrin abin da ke fita daga cikinta. Da sharrin fitintunun dare da rana, da sharrin kowane mai zuwa da dare sai dai mai zuwa da alheri, Ya Mai Rahama.
Reference: Sheikh Arnaut (Rah) yace sanadin wannan hadisin sahihi ne. Takhrij Litahabiyah (Shafi na 133)