Loading...
Language: Hausa
الم ﴿١﴾ ذَٰلِكَ الْكِتَابُ لَا رَيْبَ ۛ فِيهِ ۛ هُدًى لِّلْمُتَّقِينَ ﴿٢﴾ الَّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِالْغَيْبِ وَيُقِيمُونَ الصَّلَاةَ وَمِمَّا رَزَقْنَاهُمْ يُنفِقُونَ ﴿٣﴾ وَالَّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِمَا أُنزِلَ إِلَيْكَ وَمَا أُنزِلَ مِن قَبْلِكَ وَبِالْآخِرَةِ هُمْ يُوقِنُونَ ﴿٤﴾ أُولَـٰئِكَ عَلَىٰ هُدًى مِّن رَّبِّهِمْ ۖ وَأُولَـٰئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ ﴿٥﴾
Alif-Laam-Meem. Zaalikal-Kitaabu laa raiba feeh; hudal-lil-muttaqeen. Allazeena yu'minoona bil-ghaibi wa yuqeemoonas-Salaata wa mimmaa razaqnaahum yunfiqoon. Wallazeena yu'minoona bimaaa unzila ilaika wa maaa unzila min qablika wa bil-Aakhirati hum yooqinoon. Ulaaa'ika 'alaa hudam-mir-Rabbihim wa ulaaa'ika humul-muflihoon.
(1) Alif, Lam, Mim. (2) Wannan Littafi ne, babu shakka a cikinsa; shiriya ne ga masu taƙawa - (3) Waɗanda suke yin imani da gaibi, kuma suna tsayar da sallah, kuma suna ciyarwa daga abin da Muka azurta su. (4) Da waɗanda suke yin imani da abin da aka saukar maka, da abin da aka saukar gabaninka, kuma suna da yaƙini game da Lahira. (5) Waɗannan suna kan shiriya daga Ubangijinsu, kuma waɗannan su ne masu rabauta.
Reference: Suratul Baqarah 2: 1-5