Loading...
Language: Hausa
Daga Umm Darda (RA), ta ce wa Safwan (RA), "Shin ka yi niyyar aikin Hajji a wannan shekarar?" Na ce: "Eh." Ta ce: "Ka roƙa mana albarka, domin Manzon Allah (ﷺ) ya kasance yana cewa: Addu'ar Musulmi ga ɗan'uwansa a bayansa (wato baya nan) tana karɓuwa matuƙar yana yi wa ɗan'uwansa addu'ar alheri, sai Mala'ikan da aka wakilta ya ce: Amin, kuma ya ce: Kai ma ka samu irinsa."
Reference: Muslim: 2733