Loading...
Language: Hausa
Abu Hurairah (RA) ya ruwaito cewa Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Akwai mutane uku da ba a mayar da addu’arsu: Mai azumi lokacin da yake buɗe baki, shugaba adali, da addu’ar wanda aka zalunta; Allah yana ɗaukaka ta sama da gajimare kuma Ya buɗe mata kofofin sama. Kuma Ubangiji Ya ce: ‘Na rantse da Izzata, tabbas zan taimake ki, ko da kuwa bayan wani lokaci ne.’”
Reference: Hasan. Tirmidhi: 3598