Loading...
Language: Hausa
Annabi (ﷺ) ya ce: Mutumin da ya tashi da dare ya faɗi waɗannan kalmomi -
لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيْكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَىْءٍ قَدِيْرٌ. اَلْحَمْدُ لِلَّهِ، وَسُبْحَانَ اللَّهِ، وَلَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، وَاللَّهُ أَكْبَرُ، وَلَا حَوْلَ وَلَا قُوَّةَ إِلَّا بِاللَّهِ
Laa ilaaha illAllahu Wa'hdahu laa Sharika lahu Lahul mulku, wa lahul-'hamdu wa huwa 'alaa kulli shay'in Qadir. Alhamdulillah wa subhanallah wa laa ilaaha illAllahu wAllahu akbar wa laa 'hawla Walaa Quwata illa billah
Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Shi kaɗai yake ba shi da abokin tarayya. Mulki Nasa ne kuma dukkan yabo ya tabbata a gare Shi. Shi Mai iko ne a kan komai. Dukkan yabo na Allah ne. Tsarki ya tabbata ga Allah. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Allah ne Mafi Girma. Babu dabara kuma babu ƙarfi sai tare da Allah. Sannan ya ce: Ya Allah! Ka gafarta mani. Ko ya roƙi (Allah), za a amsa masa, kuma idan ya yi alwala (ya yi sallah), za a karɓi sallar tasa.
Reference: Bukhari: 1154