Loading...
Language: Hausa
Manzon Allah (SAW) ya ce, idan wani bawan Allah ya fuskanci wata musiba ya kuma ce:
اَللَّهُمَّ إِنِّي عَبْدُكَ وَابْنُ عَبْدِكَ وَابْنُ أَمَتِكَ نَاصِيَتِي بِيَدِكَ مَاضٍ فِيَّ حُكْمُكَ عَدْلٌ فِيَّ قَضَاؤُكَ أَسْأَلُكَ بِكُلِّ اِسْمٍ هُوَ لَكَ سَمَّيْتَ بِهِ نَفْسَكَ أَوْ عَلَّمْتَهُ أَحَدًا مِنْ خَلْقِكَ أَوْ أَنْزَلْتَهُ فِي كِتَابِكَ أَوِ اسْتَأْثَرْتَ بِهِ فِي عِلْمِ الْغَيْبِ عِنْدَكَ أَنْ تَجْعَلَ الْقُرْآنَ رَبِيْعَ قَلْبِي وَنُورَ صَدْرِي وَجَلَاءَ حُزْنِيْ وَذَهَابَ هَمِّيْ
Allaahumma 'innee 'abduka, wabnu 'abdika, wabnu 'amatika, naasiyatee biyadika, maadhin fiyya hukmuka, 'adlun fiyya qadhaa'uka, 'as'aluka bikulli ismin huwa laka, sammayta bihi nafsaka, 'aw 'allamtahu 'ahadan min khalqika, 'aw 'anzaltahu fee kitaabika, 'aw ‘ista'tharta bihi fee 'ilmil-ghaybi 'indaka, 'an taj'alal-Qur'aana rabee'a qalbee, wa noora sadree, wa jalaa'a huznee, wa dhahaaba hammee
Ya Allah, ni bawanKa ne, ɗan bawanKa, ɗan baiwarKa. Makiyata tana hannunKa (Kana yadda Ka so da ni). HukuncinKa zartacce ne a kaina, kuma ƙaddararKa adalci ce a gare ni. Ina roƙonKa da dukkan sunan da yake naKa ne, wanda Ka ambaci kanKa da shi, ko Ka sanar da shi ga wani daga halittarKa, ko Ka saukar da shi a cikin LittafinKa, ko Ka keɓe shi a cikin ilimin gaibi a wurinKa, Ka sanya Alƙur'ani ya zama nishadin zuciyata, da hasken ƙirjina, da yaye baƙin cikina, da tafiyar da damuwata. Lallai Allah zai tafiyar da damuwarsa da matsalolinsa ya musanya su da farin ciki. Aka ce: 'Ya Manzon Allah (SAW)! Ashe ba za mu koye ta ba?' Annabi (SAW) ya ce: "Tabbas! Duk wanda ya ji ta ya kamata ya koye ta."
Reference: Sahih (Albani). Silsilatul Sahiha: 199