Loading...
Language: Hausa
Abdullah ɗan Amr ɗan al-'As (RA) ya ruwaito cewa ya ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: Lallai zukatan 'yan Adam duka suna tsakanin yatsun nan biyu daga cikin yatsun Ubangiji Mai rahama kamar zuciya ɗaya. Yana juya ta zuwa duk (ɓangaren da) Ya so. Sannan Manzon Allah (SAW) ya ce:
اَللَّهُمَّ مُصَرِّفَ الْقُلُوْبِ صَرِّفْ قُلُوْبَنَا عَلَى طَاعَتِكَ
Allaahumma musarrifal-qulubi, sarrif qulubanaa 'alaa taa'atik
Ya Allah, Mai juya zuciya, Ka juya zukatanmu zuwa ga biyayya gare Ka.
Reference: Muslim: 2655