Loading...
Language: Hausa
Shahr bin Hawshab (RA) ya ce: "Na ce wa Ummu Salama (RA): 'Ya Uwar Muminai! Wace addu'a ce Manzon Allah (SAW) ya fi yawan yi lokacin da yake tare da ke?' Ta ce: 'Addu'ar da ya fi yawan yi ita ce:
يَا مُقَلِّبَ الْقُلُوبِ ثَبِّتْ قَلْبِي عَلَى دِيْنِكَ
Ya Muqallibal-qulub, thabbit qalbi 'alaa dinik
Ya Mai juya zukulata! Ka tabbatar da zuciyata a kan addininKa. 'Sai na ce: "Ya Manzon Allah (SAW), me yasa kake yawan yin addu'a cewa: (an ambaci addu'ar a sama)? Ya (SAW) ya ce: 'Ya Ummu Salama! Lallai, babu wani ɗan adam face zuciyarsa tana tsakanin Yatsu biyu na Yatsun Allah, don haka wanda Ya so sai Ya tabbatar da shi, kuma wanda Ya so sai Ya karkatar da shi.''
Reference: Sahih. Tirmidhi: 3522