Loading...
Language: Hausa
Ibnu Abbas (RA) ya ruwaito: Annabi (SAW) ya kasance yana faɗi a cikin addu'a:
رَبِّ أَعِنِّيْ وَلَا تُعِنْ عَلَىَّ وَانْصُرْنِيْ وَلَا تَنْصُرْ عَلَىَّ وَامْكُرْ لِي وَلَا تَمْكُرْ عَلَىَّ وَاهْدِنِيْ وَيَسِّرِ الْهُدَى لِي وَانْصُرْنِيْ عَلَى مَنْ بَغَى عَلَىَّ رَبِّ اجْعَلْنِيْ لَكَ شَكَّارًا لَكَ ذَكَّارًا لَكَ رَهَّابًا لَكَ مِطْوَاعًا لَكَ مُخْبِتًا إِلَيْكَ أَوَّاهًا مُنِيبًا رَبِّ تَقَبَّلْ تَوْبَتِيْ وَاغْسِلْ حَوْبَتِيْ وَأَجِبْ دَعْوَتِيْ وَثَبِّتْ حُجَّتِيْ وَسَدِّدْ لِسَانِيْ وَاهْدِ قَلْبِيْ وَاسْلُلْ سَخِيْمَةَ صَدْرِيْ
Rabbi! A'inni wa laa tu'in 'alayya, wansurni wa laa tansur 'alayya, wamkurli wa la tamkur 'alayya, wahdini wa yassiril-huda li, wansurni 'alaa man bagha 'alayya. Rabbij'alni laka shakkaran laka dhakkaran, laka rahhaban, laka mitwaa'an, laka mukhbitan, 'ilayka awwaahan muniban. Rabbi! Taqabbal tawbati, waghsil ‘hawbati wa ajib da'wati, wa thabbit hujjati, wa saddid lisaani, wahdi qalbi, waslul sakhimata sadri
Ya Ubangijina, Ka taimake ni, kada Ka taimaka a kaina, Ka ba ni nasara, kada Ka ba da nasara a kaina, Ka shirya mini (dabara), kada Ka shirya a kaina, Ka shiryar da ni kuma Ka sauƙaƙe mini shiriya, Ka ba ni nasara a kan wanda ya zalunce ni. Ya Ubangijina, Ka sanya ni mai yawan godiya gare Ka, mai yawan ambatonKa, mai yawan tsoronKa, mai yawan biyayya gare Ka, mai yawan ƙasƙanci gare Ka, mai yawan kuka da komawa gare Ka. Ya Ubangijina! Ka karɓi tubata, Ka wanke zunubina, Ka amsa addu'ata, Ka tabbatar da hujjata, Ka dre harshena, Ka shiryar da zuciyata, kuma Ka cire ƙullatar ƙirjina.
Reference: Sahih. Tirmidhi: 3551