Loading...
Language: Hausa
A'isha (RA) ta ruwaito: Manzon Allah (SAW) ya koya mata wannan addu'ar:
اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنَ الْخَيْرِ كُلِّهِ عَاجِلِهِ وَآجِلِهِ مَا عَلِمْتُ مِنْهُ وَمَا لَمْ أَعْلَمْ وَأَعُوْذُ بِكَ مِنَ الشَّرِّ كُلِّهِ عَاجِلِهِ وَآجِلِهِ مَا عَلِمْتُ مِنْهُ وَمَا لَمْ أَعْلَمْ اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ خَيْرِ مَا سَأَلَكَ عَبْدُكَ وَنَبِيُّكَ وَأَعُوْذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا عَاذَ بِهِ عَبْدُكَ وَنَبِيُّكَ اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ الْجَنَّةَ وَمَا قَرَّبَ إِلَيْهَا مِنْ قَوْلٍ أَوْ عَمَلٍ وَأَعُوْذُ بِكَ مِنَ النَّارِ وَمَا قَرَّبَ إِلَيْهَا مِنْ قَوْلٍ أَوْ عَمَلٍ وَأَسْأَلُكَ أَنْ تَجْعَلَ كُلَّ قَضَاءٍ قَضَيْتَهُ لِي خَيْرًا
Allaahumma inni as’aluka minal-khairi kullihi ‛aajilihi wa aajilihi, maa ‛alimtu minhu wa maa lam a‛lam, wa a‛oodhu bika minash-sharri kullihi ‛aajilihi wa aajilihi, maa ‛alimtu minhu wa maa lam a‛lam, Allaahumma inni as’aluka min khairi maa sa’alalka ‛abduka wa nabiyuka, wa a‛oodhu bika min sharri maa 'aadha bihi ‛abduka wa nabiyyuka, Allaahumma innee as’alukal-jannata wa maa qarraba ilayhaa min qaulin aw ‛amal, wa a'oodhu bika minan-naar, wa maa qarraba ilayhaa min qaulin aw ‛amal. wa as'aluka an taj‛ala kulla qadaa’in qaday-tahu lee khayra
Ya Allah! Ina roƙonKa dukkan alheri, na gaggawa da na jinkiri, wanda na sani daga ciki da wanda ban sani ba. Kuma ina neman tsarinKa daga dukkan sharri, na gaggawa da na jinkiri, wanda na sani daga ciki da wanda ban sani ba. Ya Allah! Ina roƙonKa alherin abin da bawanKa kuma AnnabinKa (SAW) ya roƙe Ka, kuma ina neman tsarinKa daga sharrin abin da bawanKa kuma AnnabinKa (SAW) ya nemi tsari da shi. Ya Allah! Ina roƙonKa Aljanna da abin da yake kusantarwa zuwa gare ta na magana ko aiki, kuma ina neman tsarinKa daga Wuta da abin da yake kusantarwa zuwa gare ta na magana ko aiki, kuma ina roƙonKa Ka sanya dukkan ƙaddarar da Ka ƙaddara mini ta zama alheri.
Reference: Sahih. Ibn Majah: 3846