Loading...
Language: Hausa
Ibnu Umar (RA) ya ce: Ba kasafai Manzon Allah (SAW) yake tashi daga zama ba har sai ya yi wa Sahabbansa addu'a da waɗannan kalmomi:
اَللَّهُمَّ اقْسِمْ لَنَا مِنْ خَشْيَتِكَ مَا يَحُوْلُ بَيْنَنَا وَبَيْنَ مَعَاصِيْكَ وَمِنْ طَاعَتِكَ مَا تُبَلِّغُنَا بِهِ جَنَّتَكَ وَمِنَ الْيَقِيْنِ مَا تُهَوِّنُ بِهِ عَلَيْنَا مُصِيْبَاتِ الدُّنْيَا وَمَتِّعْنَا بِأَسْمَاعِنَا وَأَبْصَارِنَا وَقُوَّتِنَا مَا أَحْيَيْتَنَا وَاجْعَلْهُ الْوَارِثَ مِنَّا وَاجْعَلْ ثَأْرَنَا عَلَى مَنْ ظَلَمَنَا وَانْصُرْنَا عَلَى مَنْ عَادَانَا وَلَا تَجْعَلْ مُصِيْبَتَنَا فِي دِيْنِنَا وَلَا تَجْعَلِ الدُّنْيَا أَكْبَرَ هَمِّنَا وَلَا مَبْلَغَ عِلْمِنَا وَلَا تُسَلِّطْ عَلَيْنَا مَنْ لَا يَرْحَمُنَا
Allaahumma-qsim lanaa min khashyatika maa ya’hulu, bainanaa wa baina ma’aasika wa min taa’atika maa tuballighunaa bihi jannataka, wa minal-yaqini maa tuhawwinu bihi ‘alainaa musibaatid-dunyaa, wa matti’naa bi-asmaa’inaa wa absarinaa wa quwwatinaa maa a’hyaytanaa, waj’alhul-waaritha minnaa, waj’al tha’ranaa ‘alaa man zalamanaa, wansurnaa ‘alaa man ‘aadaanaa, wa laa taj’al musibatanaa fi dininaa, wa laa taj’alid-dunyaa akbara hamminaa wa laa mablagha ‘ilminaa, wa laa tusallit ‘alainaa man laa yar’hamunaa
Ya Allah, Ka raba mana tsoronKa gwargwadon abin da zai shiga tsakaninmu da saɓa maKa, da biyayyarKa gwargwadon abin da zai isar da mu AljannarKa, da yaƙini gwargwadon abin da zai sauƙaƙa mana musibun duniya. Kuma Ka nishadantar da mu da j’inmu da ganinmu da ƙarfinmu matuƙar Ka rayar da mu, kuma Ka sanya shi (ƙarfin) magaji daga gare mu. Kuma Ka sanya ɗaukar fansarmu a kan wanda ya zalunce mu, kuma Ka taimake mu a kan wanda ya yi gaba da mu. Kada Ka sanya musibarmu a cikin addininmu, kuma kada Ka sanya duniya ta zama ita ce babban damuwarmu, ko ƙarshen iliminmu, kuma kada Ka tura a kanmu wanda ba zai ji tausayinmu ba.
Reference: Hasan. Tirmidhi: 3502