Loading...
Language: Hausa
Annabi (SAW) ya yi sallar asuba, bayan ya yi sallama, ya kasance yana cewa:
اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ يَا اَللَّهُ بِأَنَّكَ الْوَاحِدُ الْأَحَدُ الصَّمَدُ الَّذِي لَمْ يَلِدْ وَلَمْ يُولَدْ وَلَمْ يَكُنْ لَّهُ كُفُوًا أَحَدٌ أَنْ تَغْفِرَ لِي ذُنُوْبِيْ، إِنَّكَ أَنْتَ الْغَفُورُ الرَّحِيمُ
Allaahumma inni as'aluka yaa Allahu! Bi'annakal-Waahidul-'Ahadus-Samadul-ladhi lam yalid wa lam yoolad, wa lam yakun lahu kufuwan 'Ahad, 'an taghfirali dhunubi, 'innaka 'Antal-Ghafoorur-Raheem
Ya Allah, ina roƙonKa, Ya Allah, saboda Kai ne Guda ɗaya, Makaɗaici, Titsiye (wanda ake buƙata), wanda bai haifa ba kuma ba a haife shi ba, kuma babu wani da ya yi daidai da Shi, (ina roƙonKa) Ka gafarta mini zunubaina, lallai Kai ne Mai yawan gafara, Mai jin ƙai. Yana sauraron addu'arsa, Manzon Allah (SAW) ya ce: "An gafarta masa," sau uku.
Reference: Sahih. An-Nasa'i: 1301