Loading...
Language: Hausa
اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ بِأَنَّ لَكَ الْحَمْدُ لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ الْمَنَّانُ بَدِيْعُ السَّمَوَاتِ وَالْأَرْضِ يَا ذَا الْجَلَالِ وَالْإِكْرَامِ يَا حَيُّ يَا قَيُّومُ إِنِّي أَسْأَلُكَ
Allaahumma inni as'aluka bi-anna lakal-hamdu, laa ilaaha illaa antal-mannaanu badi'us-samawaati wal-ardi, yaa dhal-jalaali wal-ikram! Yaa ‘hayyu yaa qayyum! Inni as'aluka
Ya Allah, lallai ina roƙonKa saboda godiya ta tabbata a gare Ka, babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, Mai yawan kyauta, Mahaliccin sammai da ƙasa, Ya Mai girma da ɗaukaka! Ya Rayayye, Ya Mai tsayuwa da Kansa! Lallai ina roƙonKa. An ruwaito cewa Anas ɗan Malik (RA) ya ce: "Ina zaune tare da Manzon Allah (SAW) sai ga wani mutum yana sallah. Lokacin da ya yi ruku'u, ya yi sujada kuma ya karanta tahiya, sai ya yi addu'a, kuma a cikin addu'arsa ya ce: (An ambaci addu'ar a sama) Sannan Annabi (SAW) ya ce: 'Shin kun san abin da ya yi roƙo da shi?' Suka ce: "Allah (SWT) da ManzonSa ne suka fi sani. Ya (SAW) ya ce: 'Na rantse da Wanda raina yake HannunSa, ya roƙi Allah da Babban SunanSa, wanda idan an kira Shi da shi, Yana amsawa, kuma idan an roƙe Shi da shi, Yana bayarwa.'"
Reference: Sahih. An-Nasa'i: 1300