Loading...
Language: Hausa
Annabi (ﷺ) ya ji wani mutum yana addu'a yana cewa -
اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ بِأَنَّ أَشْهَدُ أَنَّكَ أَنْتَ اللَّهُ لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ الْأَحَدُ الصَّمَدُ الَّذِيْ لَمْ يَلِدْ وَلَمْ يُوْلَدْ وَلَمْ يَكُنْ لَهُ كُفُوًا أَحَدٌ
Allaahumma inni as-aluka bi anna ash-hadu annaka antallahu laa ilaaha illaa antal a'hadus samadulladhi lam yalid wa lam yulad wa lam yakun lahu kufuwan a'had
Ya Allah, ina roƙonKa, ta hanyar cewa na shaida cewa Kai ne Allah. Babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, Allah ɗaya tilo, wanda bai buƙatar komai daga halitta, Wanda ba a haife Shi ba kuma bai haifa ba, kuma babu wanda ya yi daidai da Shi. Sannan Annabi (ﷺ) ya ce, Ka roƙi Allah ta hanyar Babban SunanSa, wanda idan aka roƙe Shi da shi Yana bayarwa, kuma idan aka yi addu'a da shi Yana amsawa.
Reference: Sahih (Albani). Nasai: 1300