Loading...
Language: Hausa
اَللَّهُمَّ بِعِلْمِكَ الْغَيْبَ وَقُدْرَتِكَ عَلَى الْخَلْقِ أَحْيِنِي مَا عَلِمْتَ الْحَيَاةَ خَيْرًا لِيْ، وَتَوَفَّنِيْ إِذَا عَلِمْتَ الْوَفَاةَ خَيْرًا لِي، اَللَّهُمَّ وَأَسْأَلُكَ خَشْيَتَكَ فِي الْغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ وَأَسْأَلُكَ كَلِمَةَ الْحَقِّ فِي الرِّضَا وَالْغَضَبِ، وَأَسْأَلُكَ الْقَصْدَ فِي الْفَقْرِ وَالْغِنَى، وَأَسْأَلُكَ نَعِيمًا لَا يَنْفَدُ، وأَسْأَلُكَ قُرَّةَ عَيْنٍ لَا تَنْقَطِعُ، وَأَسْأَلُكَ الرِّضَا بَعْدَ الْقَضَاءِ، وَأَسْأَلُكَ بَرْدَ الْعَيْشِ بَعْدَ الْمَوْتِ، وَأَسْأْلُكَ لَذَّةَ النَّظَرِ إِلَى وَجْهِكَ، وَالشَّوْقَ إِلَى لِقَائِكَ، فِي غَيْرِ ضَرَّاءَ مُضِرَّةٍ، وَلَا فِتْنَةٍ مُضِلَّةٍ، اَللَّهُمَّ زَيِّنَّا بِزِينَةِ الْإِيمَانِ، وَاجْعَلْنَا هُدَاةً مُهْتَدِينَ
Allaahumma bi 'ilmikal-ghaiba wa qudratika 'alal-khalqi a’hyini maa 'alimtal-‘hayaata khairan li, wa tawaffani idhaa 'alimtal-wafata khairan li. Allaahumma wa as'aluka khashyataka fil-ghaibi wash-shahaadati wa as'aluka kalimatal-haqqi fir-ridaa wal ghadabi, wa as'alukal-qasda fil faqri wal-ghinaa, wa as'aluka na'iman laa yanfadu wa as'aluka qurrata ‘ainin laa tanqati'u wa as'alukar-ridaa ba'dal-qadaa'i, wa as'aluka bardal 'aishi ba'dal-mawti, wa as'aluka ladh dhatan-nazari ilaa wajhika wash-shawqa ilaa liqaa'ika fi ghayri darraa'a mudirratin, wala fitnatin mudillatin, Allaahumma zayyinnaa bizinatil-imani waj'alna hudaatam muhtadin
Ya Allah, saboda iliminKa na gaibi da ikonKa a kan halitta, Ka rayar da ni matuƙar Ka san cewa rayuwa ta fi alheri a gare ni, kuma Ka karɓi raina idan Ka san cewa mutuwa ta fi alheri a gare ni. Ya Allah, ina roƙonKa tsoronKa a ɓoye da a bayyane. Kuma ina roƙonKa faɗar gaskiya a lokacin yarda da fushi. Kuma ina roƙonKa matsakaicin hali a lokacin talauci da wadata. Kuma ina roƙonKa ni'ima da ba ta ƙarewa, da sanyin ido da ba ya yankewa. Kuma ina roƙonKa yarda bayan ƙaddara, da rayuwa mai daɗi bayan mutuwa. Kuma ina roƙonKa daɗin kallon FuskarKa da begen haɗuwa da Kai ba tare da cutarwa mai cutarwa ba ko fitina mai ɓatarwa. Ya Allah, Ka kawata mu da kawar imani kuma Ka sanya mu masu shiriya waɗanda suka shiryu. 'Ata bin As-Sa'ib (RA) ya ruwaito cewa mahaifinsa ya ce: "Ammar bin Yasir (RA) ya ja mu sallah kuma ya gupce ta. Wasu mutane suka ce masa: 'Ka gupce sallah.' Ya ce: 'Duk da haka na karanta addu'o'in da na ji daga Manzon Allah (SAW).' Lokacin da ya tashi ya tafi, wani mutum ya bi shi ya tambaye shi game da wannan addu'ar, sannan ya zo ya faɗa wa mutane: (An ambaci addu'ar a sama)
Reference: Sahih. Nasa'i: 1305