Loading...
Language: Hausa
Manzon Allah (SAW) ya kasance yana umartar mu cewa idan za mu kwanta a kan gadonmu, mu faɗi waɗannan kalmomi:
اَللَّهُمَّ رَبَّ السَّمَوَاتِ وَرَبَّ الْأَرْضِ، وَرَبَّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ، رَبَّنَا وَرَبَّ كُلِّ شَيْءٍ، فَالِقَ الْحَبِّ وَالنَّوَى، وَمُنْزِلَ التَّوْرَاةِ وَالْإِنْجِيْلِ وَالْفُرْقَانِ، أَعُوْذُ بِكَ مِنْ شَرِّ كُلِّ شَيْءٍ أَنْتَ آخِذٌ بِنَاصِيَتِهِ، اَللَّهُمَّ أَنْتَ الْأَوَّلُ فَلَيْسَ قَبْلَكَ شَيْءٌ، وَأَنْتَ الْآخِرُ فَلَيْسَ بَعْدَكَ شَيْءٌ، وَأَنْتَ الظَّاهِرُ فَلَيْسَ فَوْقَكَ شَيْءٌ، وَأَنْتَ الْبَاطِنُ فَلَيْسَ دُونَكَ شَيْءٌ، اِقْضِ عَنَّا الدَّيْنَ وَأَغْنِنَا مِنَ الْفَقْرِ
Allaahumma Rabbas-samawaati wa Rabbal ardi, wa Rabbal-'Arshil-'Adheem, Rabbanaa wa Rabba kulli shay 'in, faaliqal-habbi wannawaa, wa munzilat-Tawraati wal-'Injeeli, wal-Furqaan, 'a'oodhu bika min sharri kulli shay'in 'Anta 'aakhidhun binaasiyatihi. Allaahumma 'Antal-'Awwalu falaysa qablaka shay'un, wa 'Antal-'Aakhiru falaysa ba'daka shay'un, wa 'Antadh-Dhaahiru falaysa fawqaka shay'un, wa 'Antal-Baatinu falaysa doonaka shay'un, iqdhi 'annad-dayna wa 'aghninaa minal-faqr
Ya Allah, Ubangijin sammai da Ubangijin ƙasa, da Ubangijin Al'arshi Mai girma, Ubangijinmu, kuma Ubangijin komai, Mai tsaga ƙwayar hatsi da ƙwayar dabino, Mai saukar da Attaura da Injila da Alƙur'ani Mai rarrabewa, ina neman tsarinKa daga sharrin dukkan kome, wanda Kai ne Mai riƙe da gashin goshinsa (kana da cikakken iko a kansa). Ya Allah, Kai ne na Farko babu komai gabaninKa, kuma Kai ne na Ƙarshe babu komai bayanKa, kuma Kai ne na Zahiri babu wani abu a samanKa, kuma Kai ne na Baɗini babu wani abu a ƙashinKa. Ka biya mana bashi kuma Ka wadatar da mu daga talauci.
Reference: Muslim: 2713