Loading...
Language: Hausa
Mutum yana addu'a bayan Tashahhud -
اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ بِأَنَّ لَكَ الْحَمْدَ لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ الْمَنَّانُ، بَدِيعُ السَّمَوَاتِ وَالْأَرْضِ يَا ذَا الْجَلَالِ وَالْإِكْرَامِ، يَا حَيُّ يَا قَيُّوْمُ
Allaahumma inni as'aluka bi-anna lakal-hamda, laa ilaaha illaa antal-mannaanu badi'us-samawaati wal-ardi, yaa dhal-jalaali wal-ikraam! Yaa hayyu yaa qayyum
Ya Allah, ina roƙonKa saboda gaskiyar cewa yabo ya tabbata a gare Ka, babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, Wanda ke nuna falala da alheri, Mahaliccin Sammai da ƙasa, Ya Ubangijin Girma da Ɗaukaka, Ya Rayayye, Ya Mai wanzuwa. Sannan Annabi (ﷺ) ya ce: 'Shin kun san da me ya yi addu'a?' Suka ce: "Allah (SWT) da ManzonSa ne suka fi sani." Ya ce: 'Na rantse da Wanda a hannunSa raina yake, ya kira Allah da Babban SunanSa, wanda idan aka kira Shi da shi, Yana amsawa, kuma idan aka roƙe Shi da shi, Yana bayarwa.
Reference: Sahih (Albani). Nasai: 1300