Loading...
Language: Hausa
Daga A'isha (RA), ta ce, na ji Annabi (SAW) yana faɗi a cikin sallarsa:
اَللَّهُمَّ حَاسِبْنِيْ حِسَابًا يَسِيْرًا
Allaahumma haasibni hisaabay yasira
Ya Allah! Ka yi mini hisabi mai sauƙi. ‘A’isha (RA) ta ruwaito: Manzon Allah (SAW) ya ce, "Babu wanda za a yi wa hisabi a Ranar Tashin Kiyama, face sai ya halaka." Na ce "Ya Manzon Allah (SAW)! Ashe Allah bai ce: 'Sa'an nan game da wanda aka bai wa littafinsa a damansa, lallai zai karɓi hisabi mai sauƙi?' (84:7-8). Manzon Allah (SAW) ya ce, "Wancan (Ayar) tana nufin gabatarwa ce kawai, amma duk wanda aka binciki hisabinsa (aikinsa) a Ranar Tashin Kiyama, lallai za a azabtar da shi."
Reference: Bukhari: 6537