Loading...
Language: Hausa
اَللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي وَاهْدِنِيْ وَارْزُقْنِيْ وَعَافِنِيْ أَعُوْذُ بِاللَّهِ مِنْ ضِيْقِ الْمَقَامِ يَوْمَ الْقِيَامَةِ
Allaahummaghfir li, wahdini, warzuqni wa 'aafini. A‛oodhu billaahi min di'qil-maqaami yawmal-qiyaamah
Ya Allah, Ka gafarta mini, Ka shiryar da ni, Ka azurta ni kuma Ka ba ni lafiya. Ina neman tsari da Allah daga tsananin tsayuwa a Ranar Tashin Kiyama. Asim bin Humaid (RA) ya ce: "Na tambayi A'isha (RA) da me Annabi (SAW) yake fara Qiyamullaili (Sallar dare)? Ta ce: 'Ka tambaye ni abin da babu wanda ya taɓa tambayata kafinka. Manzon Allah (SAW) ya kasance yana kabbara (Allahu Akbar) sau goma, da hamdalah (Alhamdulillah) sau goma, da tasbihi (Subhanallah) sau goma, da tahlili (La ilaha illallah) sau goma, da istigfari (Astagfirullah) sau goma, sannan zai ce: (An ambaci addu'ar a sama)
Reference: Hasan Sahih. Nasa'i: 1617