Loading...
Language: Hausa
اَللَّهُمَّ لَكَ الْحَمْدُ كُلُّهُ، اَللَّهُمَّ لَا قَابِضَ لِمَا بَسَطْتَ، وَلَا مُقَرِّبَ لِمَا بَاعَدْتَ، وَلَا مُبَاعِدَ لِمَا قَرَّبْتَ، وَلَا مُعْطِيَ لِمَا مَنَعْتَ، وَلَا مَانِعَ لِمَا أَعْطَيْتَ. اَللَّهُمَّ ابْسُطْ عَلَيْنَا مِنْ بَرَكَاتِكَ وَرَحْمَتِكَ وَفَضْلِكَ وَرِزْقِكَ، اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ النَّعِيمَ الْمُقِيمَ الَّذِي لَا يَحُولُ وَلَا يَزُولُ. اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ النَّعِيمَ يَوْمَ الْعَيْلَةِ، وَالْأَمْنَ يَوْمَ الْحَرْبِ، اَللَّهُمَّ عَائِذًا بِكَ مِنْ سُوءِ مَا أَعْطَيْتَنَا، وَشَرِّ مَا مَنَعْتَ مِنَّا. اَللَّهُمَّ حَبِّبْ إِلَيْنَا الْإِيمَانَ وَزَيِّنْهُ فِي قُلُوبِنَا، وَكَرِّهْ إِلَيْنَا الْكُفْرَ وَالْفُسُوقَ وَالْعِصْيَانَ، وَاجْعَلْنَا مِنَ الرَّاشِدِينَ. اَللَّهُمَّ تَوَفَّنَا مُسْلِمِينَ، وَأَحْيِنَا مُسْلِمِينَ، وَأَلْحِقْنَا بِالصَّالِحِينَ، غَيْرَ خَزَايَا وَلَا مَفْتُونِينَ. اَللَّهُمَّ قَاتِلِ الْكَفَرَةَ الَّذِينَ يَصُدُّونَ عَنْ سَبِيلِكَ، وَيُكَذِّبُونَ رُسُلَكَ، وَاجْعَلْ عَلَيْهِمْ رِجْزَكَ وَعَذَابَكَ. اَللَّهُمَّ قَاتِلِ الْكَفَرَةَ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ، إِلَهَ الْحَقِّ
Allaahumma lakal ‘hamdu kulluhu, Allaahumma laa qaabidha limaa basat-ta, wa laa muqarriba limaa baa-’adta wa laa mubaa-’ida limaa qrrabta wa laa mu’tii-a limaa mana’ta wa laa maani’aa limaa a’tayta. Allaahummabsut ‘alainaa min barakaatika wa ra’hmatika wa fadhlika wa rizqika. Allaahumma inni as-alukan na’iimal muqiimalladhi laa ya’hulu wa laa yazuulu. Allaahumma inni as-alukan na’iima yawmal ‘ailati wal amna yawmal ‘harbi, Allaahumma ‘aa-idhan bika min suu-i maa a’taitanaa wa sharri maa mana’ta minnaa. Allaahumma habbib ilainal iimaana wa zayyinhu fii qulubinaa wa karrih ilainaal kufra wal fusuuqa wal ‘isyaana, waj’alnaa minar rashidin. Allaahumma tawaffana muslimin wa ah’inaa muslimiin. Wa alhiqnaa bissaalihiina ghaira khazayaa wa laa maftuuniin. Allaahumma qaatilil kafaratalla-dhiinaa yasudduuna ‘an sabiilika wa yukazzibuna rusulaka waj’al ‘alaihim rijzaka wa ‘adhaabaka. Allaahumma qaatilil kafaratalla-dhina ootul kitaaba, ilaahal haqq
Ya Allah, dukkan yabo ya tabbata a gare Ka. Ya Allah, babu mai cire abin da Ka shimfiɗa kuma babu mai kusantar da abin da Ka nisantar. Babu mai nisantar da abin da Ka kusantar. Babu mai bayar da abin da Ka hana kuma babu mai hana abin da Ka bayar. Ya Allah, Ka shimfiɗa a gare mu daga albarkarKa, da rahamarKa da falalarKa da arzikinKa! Ya Allah, ina roƙonKa ni'ima mai dorewa wacce ba ta canzawa ko gushewa. Ya Allah, ina roƙonKa ni'ima a Ranar tsananin talauci da aminci a Ranar Tsoro. Ya Allah, ina neman tsarinKa daga sharrin abin da Ka ba mu. Ya Allah, Ka sanya mu so imani kuma Ka kawata shi a cikin zukatanmu. Ka sanya mu ƙi kafirci, da ɓata da saɓo. Ka sanya mu a cikin shiryayyu. Ya Allah, Ka karɓi ranmu muna Musulmai da Ka rayar da mu muna Musulmai kuma Ka haɗa mu da salihai, ba tare da mun wulakanta ba ko mun fitinu. Ya Allah, Ka yaƙi kafirai waɗanda suke tare hanyaTa kuma suke ƙaryata ManzanninKa. Ka sanya wulakancinKa da azabarKa a kansu. Ya Allah, Ka yaƙi kafirai waɗanda aka bai wa Littafi, Ya Ubangijin Gaskiya! Rifa'a az-Zurqi (RA) ya ce, "A Yaƙin Uhudu lokacin da mushirikai suka ja da baya, Manzon Allah (SAW) ya ce, 'Ku tsaya a saffun domin in yabi Ubangijina Mai iko.' Suka tsaya a saffun a bayansa. Ya ce: (An ambaci addu'ar a sama)
Reference: Sahih. Adabul Mufrad: 699