Loading...
Language: Hausa
اَللَّهُمَّ حَبِّبْ عُبَيْدَكَ هَذَا وَأُمَّهُ إِلَى عِبَادِكَ الْمُؤْمِنِينَ وَحَبِّبْ إِلَيْهِمُ الْمُؤْمِنِيْنَ
Allaahumma habbib 'ubaidaka hadha wa ummahu ilaa 'ibadikal mu'minin, wa habbib ilayhimul mu'minin
Ya Allah, Ka sanya soyayyar waɗannan bayin NaKa, wato Abu Huraira da mahaifiyarsa, a cikin zukatan bayi muminai kuma Ka cika zukatansu da soyayyar bayi muminai. Na fito ina mai matuƙar farin ciki da addu'ar Manzon Allah (SAW) kuma da na zo kusa da ƙofar sai aka kulle ta daga ciki. Mahaifiyata ta ji motsin tafiyata sai ta ce: Abu Huraira, tsaya. Sai na ji karar zubar ruwa. Ta yi wanka ta saka tufafi ta yi saurin rufe kanta da mayafi ta buɗe ƙofar sannan ta ce: Abu Huraira, na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne (SAW). Shi (Abu Huraira) ya ce: Na koma wurin Manzon Allah (SAW) kuma (a wannan karon) ina zubar da hawayen farin ciki. Na ce: Manzon Allah, yi farin ciki, domin Allah Ya amsa addu'arka kuma Ya shiryar da mahaifiyar Abu Huraira. Shi (Annabi mai tsira) ya yabi Allah, kuma ya ɗaukaka Shi ya faɗi kalamai na alheri. Na ce: Ya Manzon Allah (SAW), roƙi Allah domin Ya sanya soyayyata da ta mahaifiyata a cikin zukatan bayi muminai kuma Ya cika zukatanmu da soyayyarsu, sai Manzon Allah (SAW) ya ce: (An ambaci addu'ar a sama). (Abu Huraira ya ce: Wannan addu'ar) Allah Ya karɓe ta sosai ta yadda babu wani mumini da aka haifa wanda ya ji labarina kuma ya gan ni face ya ƙaunace ni.
Reference: Muslim: 2491