Loading...
Language: Hausa
أَمْسَيْنَا وَأَمْسَا الْمُلْكُ لِلَّهِ، وَالْحَمْدُ لِلَّهِ، لَا إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، رَبِّ أَسْأَلُكَ خَيْرَ مَا فِي هَذِهِ اللَّيْلَةِ وَخَيْرَ مَا بَعْدَهَا، وَأَعُوْذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا فِي هَذِهِ اللَّيْلَةِ وَشَرِّ مَا بَعْدَهَا، رَبِّ أَعُوْذُ بِكَ مِنَ الْكَسَلِ وَسُوْءِ الْكِبَرِ، رَبِّ أَعُوْذُ بِكَ مِنْ عَذَابٍ فِي النَّارِ وَعَذَابٍ فِي الْقَبْرِ
Amsaynaa wa'amsal-mulku lillaahi walhamdu lillaahi, laa 'ilaaha 'illAllahu wahdahu laa shareeka lahu, lahul-mulku wa lahul-hamdu wa Huwa 'alaa kulli shay'in Qadeer. Rabbi 'as'aluka khayra maa fee haathihil-laylati wa khayra maa ba'daha wa 'A'oodhu bika min sharri maa fee haathihil-laylati wa sharri maa ba'daha, Rabbi 'A'oodhu bika minal-kasali, wa soo'il-kibari, Rabbi 'A'oodhu bika min 'athaabin fin-naari wa 'athaabin fil-qabr.
Mun shiga yamma kuma mulki ya tabbata ga Allah, kuma dukkan yabo na Allah ne. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai, ba Shi da abokin tarayya, mulki Nasa ne kuma yabo Nasa ne kuma Shi Mai iko ne a kan komai. Ya Ubangijina, ina roƙonKa alherin wannan dare da alherin abin da ke bayansa kuma ina neman tsari daga gare Ka daga sharrin wannan dare da sharrin abin da ke bayansa. Ya Ubangijina, ina neman tsari daga gare Ka daga kasala da mummunan tsufa. Ya Ubangijina, ina neman tsari daga gare Ka daga azaba a cikin Wuta da azaba a cikin kabari. Abdullah dan Mas'ud (RA) ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya kasance yana karanta addu'ar da aka ambata a sama a kowace safiya da yamma. Da safe yana cewa Asba’hna... kuma da yamma yana cewa Amsaina maimakon Asba’hna.
Reference: Muslim: 2723