Loading...
Language: Hausa
اَللَّهُمَّ لَا طَيْرَ إِلَّا طَيْرُكَ، وَلَا خَيْرَ إِلَّا خَيْرُكَ، وَلَا إِلَهَ غَيْرُكَ
Allaahumma laa tayra 'illaa tayruka, wa laa khayra 'illaa khayruka, wa laa 'ilaaha ghayruka
Ya Allah babu shu'umci sai shu'umcinKa (abin da Ka ƙaddara), babu alheri sai alherinKa, kuma babu abin bautawa da gaskiya sai Kai. [1] Sai dai, Annabi (SAW) ya kasance yana son kyakkyawan fata. Shi ya sa lokacin da ya ji kyakkyawar kalma ko kyakkyawar magana daga mutum, ya so ta kuma ya ce, Na karɓi kyakkyawar maganarka daga bakinka. [2]
Reference: [1] Sahih (Albani). Ahmad: 7045 [2] Abu Dawud: 3719, Ahmad: 9040. Duba kuma Al-Albani, Silsilatul-'Ahadith As-Sahihah 2/363, kuma yana tare da Abu Ash-Shaikh Al-Asfahani a cikin 'Akhlaqun-Nabiyy, shafi na 270.