Loading...
Language: Hausa
Annabi (SAW) ya ce: "Duk wanda ya yi salati ɗaya a gare ni, Allah zai yi masa salati goma." [1] Ya (SAW) kuma ya ce: "Kada ku sanya kabarina ya zama wurin biki na yau da kullum. Ku yi salati a gare ni, domin lallai salatinku yana isa gare ni duk inda kuke." [2] Ya (SAW) kuma ya ce: "Marowaci shi ne wanda idan aka ambace ni a wurinsa, ya kasa yi mini salati." [3] Ya (SAW) kuma ya ce: 'Allah Yanada mala'iku waɗanda suke kewaya duniya suna isar da sallama gare ni daga al'ummata.' [4] Ya (SAW) kuma ya ce: ''Duk lokacin da wani ya yi sallama a gare ni, Allah yana dawo da raina gare ni domin in amsa sallama ga wannan mutumin. [5]
Reference: [1] Muslim: 384 [2] Sahih (Albani). Abu Dawud: 2042 [3] Sahih (Albani). Tirmidhi: 3546 [4] Sahih (Albani). Nasai: 1282 [5] Hasan (Albani). Abu Dawud: 2041