Loading...
Language: Hausa
Annabi (SAW) ya ƙara da cewa: Mutumin da ya ce:
أَسْتَغْفِرُ اللَّهَ الْعَظِيمَ الَّذِي لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ وَأَتُوبُ إِلَيهِ
Astaghfirullaahal-'Adheemal-ladhee laa 'ilaaha 'illaa Huwal-Hayyul-Qayyoomu wa 'atoobu 'ilayhi
Ina neman gafarar Allah, wanda babu abin bautawa da gaskiya sai Shi, Rayayye, Mai tsayuwa da Kansa da tallafar kowa, kuma ina tuba zuwa gare Shi. Allah zai gafarta masa ko da kuwa shi ne wanda ya gudu yayin da runduna take gaba." [1] Ya (SAW) ya ce: "Mafi kusa da Ubangiji yake zuwa ga bawanSa shi ne a tsakiyar dare, don haka idan za ku iya zama daga cikin masu ambaton Allah a wannan lokacin, to ku kasance." [2] Ya (SAW) kuma ya ce: "Mafi kusa da bawa yake ga Ubangijinsa shi ne lokacin da yake sujada, don haka ku yawaita addu'a a cikinta." [3] Ya (SAW) kuma ya ce: "Lallai zuciyata tana shagala, kuma lallai ina neman gafarar Allah sau ɗari a rana." [4]
Reference: [1] Sahih. Abu Dawud 1517 [2] Sahih. Tirmidhi 3579 [3] Muslim 482 [4] Muslim 2702