Loading...
Language: Hausa
اَلسَّلَامُ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَةُ اللَّهِ وَبَرَكَاتُهُ
As-salaamu 'alaykum wara'hmatullaahi wa barakaatuh
Aminci ya tabbata a gare ku, da Rahamar Allah da AlbarkarSa. Wani mutum ya zo wurin Annabi (SAW) ya ce: Assalamu alaikum! Ya amsa sallamarsa. Sannan ya zauna. Annabi (SAW) ya ce: Goma. Wani mutum ya zo ya ce: Assalamu alaikum warahmatullah! Ya amsa sallamarsa lokacin da ya zauna. Ya ce: Ashirin. Wani mutum ya zo ya ce: Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh! Ya amsa masa kuma ya ce lokacin da ya zauna: Talatin.
Reference: Sahih. Abu Dawud: 5195