Loading...
Language: Hausa
بِسْمِ اللَّهِ وَاللَّهُ أَكْبَرُ اَللَّهُمَّ إِنَّ هَذَا مِنْكَ وَلَكَ اَللَّهُمَّ تَقَبَّلْ مِنِّي
Bismillaahi wallaahu akbar, allaahumma inna haadha minka walak, allaahumma taqabbal minni.
Ina yanka da sunan Allah. Kuma Allah ne Mafi Girma. Ya Allah! Wannan daga gare Ka ne kuma don Kai ne. Ya Allah! Ka karɓa mini. Idan a madadin iyali ne, sai a ƙara Wamin Ahli Baiti bayan ‘Takabbal Minni’. Idan layyar ta wani ce ko kuma dabba ce ta Aƙiƙa, sai a ambaci sunan wannan mutumin ko yaron bayan ‘Takabbal Min’. A fili yake cewa babu wata ƙarin Addu'a a kan wannan batu da ta tabbata.
Reference: Irwa'ul-Ghalil: 1118