Loading...
Language: Hausa
Annabi (SAW) ya yi sallar asuba, bayan ya yi Sallama, sai ya ce:
اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ يَا اَللَّهُ بِأَنَّكَ الْوَاحِدُ الْأَحَدُ الصَّمَدُ الَّذِي لَمْ يَلِدْ وَلَمْ يُولَدْ وَلَمْ يَكُنْ لَّهُ كُفُوًا أَحَدٌ أَنْ تَغْفِرَ لِي ذُنُوْبِيْ، إِنَّكَ أَنْتَ الْغَفُورُ الرَّحِيمُ
Allaahumma inni as'aluka yaa Allahu! Bi'annakal-Waahidul-'Ahadus-Samadul-ladhi lam yalid wa lam yoolad, wa lam yakun lahu kufuwan 'Ahad, 'an taghfirali dhunubi, 'innaka 'Antal-Ghafoorur-Raheem
Ya Allah, ina roƙonKa, Ya Allah, domin Kai ne Guda ɗaya, Makaɗaici, Samad (Wanda ake buƙatarSa ba Ya buƙatar kowa), Wanda bai haifa ba kuma ba a haife Shi ba, kuma babu wani wanda ya yi daidai da Shi, Ka gafarta mini zunubaina, lallai Kai ne Mai Gafara, Mai Jin Ƙai. Yana sauraron addu'arsa, Manzon Allah (SAW) ya ce: "An gafarta masa," sau uku.
Reference: Sahih. An-Nasa'i: 1301