Loading...
Language: Hausa
An ruwaito daga Abu Musa Ashari (RA), Annabi (SAW) ya kasance yana karanta wannan addu'a:
اَللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي خَطِيْئَتِيْ وَجَهْلِيْ وَإِسْرَافِي فِي أَمْرِيْ وَمَا أَنْتَ أَعْلَمُ بِهِ مِنِّي اَللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي جِدِّيْ وَهَزَلِيْ وَخَطَئِيْ وَعَمْدِيْ وَكُلُّ ذَلِكَ عِنْدِيْ اَللَّهُمَ اغْفِرْ لِي مَا قَدَّمْتُ وَمَا أَخَّرْتُ وَمَا أَسْرَرْتُ وَمَا أَعْلَنْتُ وَمَا أَنْتَ أَعْلَمُ بِهِ مِنِّي أَنْتَ الْمُقَدِّمُ وَأَنْتَ الْمُؤَخِّرُ وَأَنْتَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيْرٌ
Allahumm-aghfir li khati'ati, wa jahli, wa israafi fi amri, wa maa Anta a'lamu bihi minni. Allahumm-aghfir li jiddi wa hazali, wa khata'i wa 'amdi, wa kullu dhalika 'indi. Allahumm-aghfir li maa qaddamtu wa maa akhkhartu, wa maa asrartu, wa maa a'lantu, wa maa Anta a'lamu bihi minni. Antal-Muqaddimu, wa Antal-Mu'akhkhiru; wa Anta 'alaa kulli shai'in Qadir
Ya Allah, Ka gafarta mini kurakuraina, da jahilcina, da wuce gona da iri a cikin lamurana. Kuma Kai Ka fi ni sanin (al'amarina). Ya Allah, Ka gafarta mini (laifukan da na aikata) da gaske ko akasin haka (da waɗanda na aikata bisa kuskure da waɗanda na yi da gangan). Duk waɗannan (kurakurai) suna tare da ni. Ya Allah, Ka gafarta mini laifin da na gabatar ko na jinkirta, wanda na ɓoye ko na bayyana, da abin da Ka fi ni sani game da su. Kai ne na Farko kuma Kai ne na Karshe kuma Kai Mai Iko ne a kan komai.
Reference: Muslim: 2719