Loading...
Language: Hausa
Wani mutum ya zo wurin Manzon Allah (SAW), ya ji shi yana cewa: "Ya Manzon Allah (SAW), me zan ce idan ina roƙon Allah?" Ya (SAW) ya ce: "Ka ce:
اَللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي وَارْحَمْنِيْ وَعَافِنِيْ وَارْزُقْنِيْ
Allaahumma-ghfir li warhamni wa 'aafini warzuqni
Ya Allah, Ka gafarta mini, Ka yi mini rahama, Ka tsare ni kuma Ka azurta ni. Kuma ya ware yatsunsa huɗu banda babban yatsa kuma ya ce: "Waɗannan za su haɗa maka al'amuran addininka da na duniya."
Reference: Sahih. Ibn Majah: 3845