Loading...
Language: Hausa
An ruwaito daga Al-Hasan ibn Ali (RA): Manzon Allah (ﷺ) ya koya mani wasu kalmomi da nake fada a lokacin witr -
اَللَّهُمَّ اهْدِنِيْ فِيمَنْ هَدَيْتَ وَعَافِنِي فِيمَنْ عَافَيْتَ وَتَوَلَّنِيْ فِيمَنْ تَوَلَّيْتَ وَبَارِكْ لِي فِيمَا أَعْطَيْتَ وَقِنِي شَرَّ مَا قَضَيْتَ فَإِنَّكَ تَقْضِي وَلَا يُقْضَى عَلَيْكَ إِنَّهُ لَا يَذِلُّ مَنْ وَالَيْتَ وَلَا يَعِزُّ مَنْ عَادَيْتَ تَبَارَكْتَ رَبَّنَا وَتَعَالَيْتَ
Allahum-mahdinee feeman hadayta, wa 'aafinee feeman 'aafayta, wa tawallanee feeman tawallayta, wa baarik lee feemaa 'a'atayta, wa qinee sharra maa qadhayta, fa'innaka taqdhee wa laa yuqdhaa 'alayka, 'innahu laa yadhillu man waalayta, wa laa ya 'izzu man 'aadayta, tabaarakta Rabbanaa wa ta'aalayta
Ya Allah, Ka shiryar da ni tare da wadanda Ka shiryar, kuma Ka ba ni lafiya tare da wadanda Ka ba lafiya. Ka kula da ni tare da wadanda Ka kula da su. Ka yi mini albarka a cikin abin da Ka bayar. Ka kare ni daga sharrin abin da Ka hukunta. Lallai Kai ne Kake hukunci kuma ba a hukunci a kanKa, kuma lallai wanda Ka jibinci lamarinsa ba zai wulakanta ba, kuma wanda Ka yi gaba da shi ba zai daukaka ba. Tsarki ya tabbata a gare Ka Ubangijinmu kuma Ka daukaka.
Reference: Sahih (Albani). Abu Dawud: 1425